Ranar Ma’aikata : Ganduje ya karawa Malaman Makaranta Shekarun Ritaya daga aiki

Date:

Daga Nafisa Abdulaziz

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullah Umar Ganduje yace gwamnatin jihar Kano ta Kara wa’adin kammala aiki ga Malaman Makaranta a jihar Kano daga Shekaru 35 zuwa 40 ,sai Kuma wa’adin Shekaru ga Malaman daga Shekaru 60 zuwa Shekaru 65.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron tunawa da Karrama Ma’aikata ta bana ,Wanda ya gudana a gidan Gwamnatin Kano.

Ganduje yace Malaman Makaranta a Kano suna bada gudunmawa sosai wajen cigaba jihar Kano, ta fuskar jajircewa wajen Ilimantar da al’ummar Kuma Ilimi ne jigon cigaban kowacce al’umma.

Yace gwamnatin Tarayya ta Kara wa’adin Ritayar ga malam Makarantun ne domin Kara musu kaimi wajen cigaba da hidimtawa al’ummar jihar Kano.

“Daga Yanzu Malaman Makaranta na Firamare da Sakandire da Makarantun gaba da Sakandire zasu Rika kammala aikin daga Shekaru 40 Mai makon Shekaru 35. Sai Kuma Wa’adin Ritayar na Shekaru Maimakon Shekaru 60 Yanzu Malaman Makaranta zasu Rika yin Ritayane idan sun Cika Shekaru 65 da kammala aiki”. Inji Ganduje

Gwamna Ganduje yace gwamnatinsa tana iya Bakin kokarin ta wajen kyautatawa Ma’aikata a jihar Kano.

Yayin taron Shugaban Kungiyar kwadago na jihar Kano Kwamared Kabiru Ado Minjibir bayan ya yabawa gwamnatin jihar Kano ya Kuma bukaci gwamnatin data bisa Ma’aikata hakkokinsu da Kuma biyan hakkokin Ma’aikatan da Suka kammala aiki.

Kadaura24 ta rawaito cewa Yayin taron an karrama Wasu Ma’aikata Masu kwazo a jihar Kano domin Kara musu kwarin gwiwar gudanar da aikin su.

5 COMMENTS

    • Masha Allah hakamma yayi daidai sukuma malami saisu qara dagewa suqara bada qaimi da himma Dan sauke nauyin al.umma da Allah ya doramusu shikuma ganduje abinda yay Allah yasaka da alkhairi by ummah labaran Muhammad gwammaja 08068429968

  1. Gaskiya hakan yayi daidai duba da namijin qoqarin da malaman makaranu sukeyi wajen gina al,umma da tarbiyya da rayuwar al,umma,malamai sune tushen duk wani alkhairi,allah ya tabbarar da alkhairi

  2. Masha Allah
    Saura albashin malaman firamare wanda har yanzu ba’a saka su cikin jerin ma’aikata masu rabauta da mafi karancin albashin 30,600 ba.

  3. Ba Kara shekaru ne ya dace ba , Kara musu albashi , da basu gratuities dinsu akan lokacine ya dace, amma wannna kashe su ne ,idan mutum ya gama aikin zai mori ragowar karfin sa , yin hakan an Kara kasara sune da iyalansu , Allah ka kawo ma malam makaranta dauki , Shekara wajen 5 , ba gratuity.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...