Daga Kamal Yakubu Ali
Shugaban Kungiyar samarin Tijjaniyya na kasa Sheikh Barrister Habib Dan Almajiri ya bukaci al’umma dasu zage damtse wajan yawaita karatun alqur’ani da kuma addu’o’i domin samun biyan bukatu agun Allah madaukakin sarki sarki da nemawa Kasar nan Zaman lafiya Mai dorewa .
Sheikh Dan Almajiri a bayyana cewa wadannan kwanaki da muke ciki na Azimin watan Ramadanu kwanaki masu tsada , wanda ya kamata kowanne musulmi ya yi amfani dashi wajan Neman yardar agun Allah madaukakin sarki .
Yace Ramadan lokacine da ake shuka ayyukan alkhairi Wanda sakamakon ayyukan ke zuwa ba tare da bata lokaci ba , adon haka ya bukaci al’ummar musulmi dasuyi amfana da wadannan kwanaki masu albarka yadda ya dace .
Shugaban Kungiyar Samarin Tijjaniyyar na Kasa yace a Wannan lokacin ya Kanata al’ummar musulmi su dukufa wajen nemawa Kasar nan Zaman lafiya Sakamakon Matsalolin tsaro da ake fuskanta a Nigeria.
Allh jikanta darahama