MatsalarTsaro :Gwamnatin jihar Kano ta bada Umarnin rufe Kwalejin Fasaha ta Bagauda

Date:

 Daga Nasiba Rabi’u Yusuf


 Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe Kwalejin Fasaha ta Bagauda ba tare da bata lokaci ba.


  Kwamishinan Ilimi na jihar, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya sanar da cewa rufe kwalejin ya zama tilas biyo bayan wani rahoton tsaro da gwamnati ta samu da kuma bukatar kare rayukan dalibai, malamai da sauran ma’aikatan kwalejin.


 Cikin Wata sanarwa da Jami’in Hulda da jama’a na Ma’aikatar Ilimi Aliyu Yusuf ya aikowa Kadaura24 yace Kwamishinan ya bukaci iyaye da su hanzarta kwashe yaransu daga Kwalejin kuma su jira karin umarnin.


 Kwamishinan yayi amfani da damar don nuna godiyar gwamnatin jihar ga iyaye bisa goyan baya da hadin kai kan manufofi da umarnin gwamnati musamman kan al’amuran da suka shafi tsaro.

15 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...