Sallah: Ku Kwashe kayanku daga kan Hanya Don Gudun Cinkoso a Kasuwarmu-Shugaban Kofar Wambai

Date:

Daga Rabi’u Usman

Shugaban Kungiyar yan Kasuwar Kofar Wambai Alhaji Kabiru M Abubakar tsamiyar Mariri yayi Kira da Jan Hankali ga Kafatanin ‘yan Kasuwar Kofar Wambai dasu Kasance Masu Bin Doka da Oda Wajen Matsar da Kayan Su Daga Kan Hanya Kasancewar yanzu Lokaci ne na Cikar Kasuwanni Musamman lokacin da Jama’a Suke Zuwa Siyan Kayan Bukatar Sallah Karama da Muke Gab da Karkare Azumin Watan Ramadana Mai Albarka.

Kabiru yayi Kiran ne yayin da yake Ganawa da Manema Labarai a Wannan Rana, yana Mai Cewar, ta Haka ne Za’a Samu Damar Dakume Mutanen da Suke Shiga Kasuwanni da Zummar yin Siyayya daga Bisani Sai Su Bige da Satar Kayan Jama’a.

Ya Kara da cewa, tuni Sun Kafa Wani Kwamatin da Zai Dinga Zagayawa Domin Duba Halin da Kasuwar take Ciki da Kuma Wadanda Suka bi Umarnin da Kuma Hukunta Masu Kunnen Kashi da Dokar da Kasuwar ta Shimfida.

Sannan yace Sun Hada Kai da Jami’an tsaro na yan Sanda, Vigilantee, Karota, da Jami’an tsaro na Farin Kaya.

A Karshe dai Shugaban yayi Kira ga Al’umma Musamman Masu Mu’amalantar Kasuwar ta su dasu Kasance Masu Bin Dokokin da Shugabancin Kasuwar ta Sanya Su Kuma Kasancewar Masu Jin Tsohon Allah a Duk Al’amuran Su na Cinikayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...