Har Yanzu Muna kan bakarmu na samar da Jirgin Kasa Mai amfani da lantarki a Kano – Ganduje

Date:

Daga Siyama Ibrahim Sani

Gwamnatin jihar Kano tace tana nan akan bakarya na Samar da jirgin Kasa irin na zamani Mai amfani da lantarki Wanda Zai rika gudanar da harkokinsa a birnin Kano da Kewaye.

Gwamna Dr Abdullah Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da ya shirya Buda Baki da Yan Kasuwar jihar nan a cigaba da jerin tarukan Shan ruwa da yake yi da rukunonin al’umma daban-daban.

Gwamna Ganduje yace har Yanzu suna cigaba da Tattaunawa da Wasu kamfanoni a Kasar China wadanda sune zasu gudanar da aikin titin jirgin Wanda yace Zai taimaka wajen Kara bunkasa harkokin Kasuwanci a Kano.

Yace gwamnatin jihar Kano tana iya bakin kokarin ta wajen inganta harkokin Kasuwanci a jihar Kano ta hanyar Samar da tituna da hada hannu da Yan Kasuwa a fannoni daban-daban domin cigaban Kasuwanci a jihar Kano.

“Mun Samar da Na’urorin Tsaro Sannan Muna aikin hadin gwiwa da Hukumomin Tsaro a Kano domin sai da Tsaro ne ake iya Kasuwanci a ko’ina a fadin Duniya”. Ganduje

Yace gwamnatinsa ta dage wajen ganin an sake Bude filin jirgin saman malam Aminu Kano saboda barinsa a rufe Yana gurgunta Kasuwanci, don akwai Yan Kasuwa a Kano da suke tafiya kasashen waje domin harkokinsu na Kasuwanci.

Kadai ta rawaito cewa Gwamna Ganduje ya bukaci hadin Jan yan Kasuwar domin yace gwamnati ita kadai bazata iya wadata kowa da komai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...