Mal. Ibrahim Khalil ya bayyana yadda zai magance kura-kuran Shekarau, Kwankwaso da Ganduje idan ya zama gwamnan kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADC, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana rashin bin doka da oda a matsayin babbar matsalar da take kawo cin hanci da rashawa.

 Sheikh Ibrahim ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da kungiyar wakilan kafafen yada labaran ta kano suka shirya .
 A cewarsa, cin hanci da rashawa da sauran matsalolin sun samo asali ne daga rashin bin doka da oda da ke hana ci gaba .
Talla
 Sheikh Ibrahim Khalil ya jaddada cewa idan aka zabe shi gwamnatinsa za ta tabbatar da bin doka da oda da inganta muhalli da lafiya da ilimi da kuma bunkasar tattalin arziki.
 “Idan mutane suka bi doka da oda za a magance yawancin matsalolinmu ciki har da cin hanci da rashawa”.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
 Ya kara da cewa, tuntubar juna, saukakawa, samar da damammaki, da zaburar da jama’a, zai taimaka matuka wajen shimfida hanyoyin da shugabanni za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
 Dan takarar gwamnan na ADC ya kara da cewa, idan ya sami damar zama gwamna, jihar Kano za ta ci moriyar gwamnati ta hanyar shugabanci nagari, hadin kai da sadaukarwa.
 Sheikh Ibrahim Khalil ya jaddada cewa, ba ya tsoron duk wani dan siyasa a jihar, yana mai cewa shi ne ya fi kowa cancanta da zai iya mulkin Kano sakamakon kura-kuran da wasu tsofaffin gwamnoni suka yi a baya.
 Ya kuma yi watsi da zargin cewa yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.
 Dan takarar gwamnan ADC ya nuna cewa, ba ya goyon bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a yanzu, har sai kotu ta yanke hukunci kan karar da ta shafi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsu, Dumebi Kachukwu.
 Sheikh Ibrahim Khalil ya ci gaba da bayanin cewa, idan kotu ta yanke hukunci kan dan takarar shugaban kasa za su mara masa baya, kuma idan kotu ta bayyana cewa jam’iyyar ba ta da dan takarar shugaban kasa, to za su yanke shawarar wanda za su mara wa baya a cikin sauran ‘yan takarar shugaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki – Ministan lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta...

Sarkin Hausawan Arewa, Amb. Balarabe Tatari, Ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Buhari da Dantata

Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Alhaji Balarabe...

INEC ta sanya ranar fara rijistar masu zabe a Nigeria

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan...