Abubuwan da ya kamata ku sani game da sabuwar cutar da ke yaduwa a Kano da Legos

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta tabbatar da samun bullar wata cuta mai tsanani a cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar ranar Juma’ar data gabata, inda ta ce ta dauki matakan kula da wadanda suka kamu da cutar a jihohin da aka ambata yayin da a halin yanzu ake sa ido kan wasu jihohin.

 

 

A cewar Darakta Janar na Hukumar ta NCDC, Dokta Ifedayo Adetifa, hukumar na sanya idanu sosai kan cutar Diphtheria a jihohin Osun da Yobe inda a yanzu haka ake samun karuwar masu kamuwa da cutar.

 

 

A cikin shawarwarin da safiyar Juma’a, Adetifa ya ce baya ga wadanda ake zargi sun kamu da cutar, akwai kuma wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a dakin gwaje-gwaje, kuma suna aiki tare da ma’aikatun lafiya na jihohi da abokan hulda domin sa ido da kuma dakile sake yaduwar cutar.

Talla

 

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa a ranar Juma’a ta tabbatar da rahoton bullar cutar diphtheria a jihohin Legas da Kano.

 

 

Diphtheria cuta ce mai saurin yaduwa, ta hanyar kwayar cuta mai suna Corynebacterium diphtheriae wacce ke yin shiga jikin mutane wacce take cutar da mutane matuka.

 

 

Cutar ta shafi hanci, makogwaro, da kuma fatar jikin mutum a wasu lokutan.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

 

Diphtheria tana kashe kananan yara sosai .

 

Daga bullar cutar zuwa ranar 13 ga watan Janairu, cutar ta kashe a kalla mutane 25, inda ake zargin mutane 58 ne suka kamu da cutar a jihar Kano.

 

 

Bayanai daga NCDC sun nuna cewa an samu bullar cutar a jihar Borno a shekarar 2011 inda jimillar mutane 98 suka kamu da cutar, kuma mutane 21 sun mutu ( adadin wadanda suka mutu ya kai kashi 21.4 cikin dari).

 

 

Hakanan, a cikin shekarun 2018 da 2019, an ba da rahoton cikin mutane 2,289 akalla mutane 1,870 aka tabbatar sun kamu da cutar.

 

 

 

Cutar tana yaduwa

 

 

Kwayoyin cutar diphtheria suna yaduwa tsakanin mutane, yawanci ta hanyar numfashi, tari ko atishawa. Hakanan mutane na iya yin kamuwa ta hanyar taɓa tufafin wadanda suka kamu da cutar, ko taba wani abu da mai cutar ya taba da dai sauransu.

 

 

Hadarin da cutar take da shi

 

 

Mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar diphtheria yara ne da manya waɗanda ba su karɓi allurar pentavalent ba (alurar rigakafi mai ɗauke da diphtheria toxoid).

 

 

Wasu da ke cikin haɗari kamuwa da cutar sune mutanen da ke zaune a cikin cunkoson jama’a, mutanen da ke zaune a wuraren da ke da ƙarancin tsafta, ma’aikatan kiwon lafiya, da sauran waɗanda suke zaune da wadanda ake zargi sun kamu da cutar ta diphtheria.

 

 

Yadda za a yi Rigakafin, da Kuma magance ta

 

 

Hukumar NCDC ta ce dole ne abi jadawalin rigakafin yara a Najeriya, wanda ake bada shawarar yin allurai uku na allurar rigakafin pentavalent ga yara a mako na 6, 10, da 14 na rayuwar yara

 

 

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce allurar rigakafin cutar diphtheria tana rage yawan mace-mace da cutar diphtheria take haifarwa sosai, duk da haka, diphtheria har yanzu babbar matsalar ce ga yara a kasashen da ke fama da karancin allurar rigakafin yara na yau da kullun.

 

akwai Kuma nau’ikan allurai da ake iya amfani da su wajen maganin cutar ga wadanda suka kamu da cutar Babba ko yaro.

 

 

 

Wani kwararre kan cututtuka a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas da ke Idi-Araba, Legas, Dokta Iorhen Akase ya ce, “A matsayin kasa, babban abin da ya kamata a yi shi ne a kara yawan allurar rigakafin domin rigakafin DPT na daya daga cikin alluran rigakafin da ake baiwa yara a cikin jerin alluran rigakafi da ake yi musu.

 

 

 

Shawarar NCDC ga ‘yan Najeriya

 

 

Don rage haɗarin cutar diphtheria a cikin kasa.

 

 

1. Ya kamata iyaye su tabbatar da cewa an yi wa yaransu cikakkiyar allurar rigakafin cutar diphtheria tare da allurai uku na allurar rigakafin pentavalent kamar yadda aka ba da shawarar a cikin jadawalin rigakafin yara.

 

2. Ma’aikatan kiwon lafiya ya kamata su kula da babban ginshiƙi na alamun diphtheria watau, kula da kuma duba alamun diphtheria.

 

3. Mutanen da alamun cutar diphtheria suka bayyana a jikin su, ya kamata su kebe kansu, a Kuma gaggata sanar da jami’an lafiya mafi kusa da kuma sanar da NCDC ta hanyar kiran layin kar ta kwana na (6232) wanda kiransa na kyauta.

 

 

4. Ya kamata a kula da kusancin abokan hulɗa tare da tabbatar da yanayin diphtheria a hankali idan aka ba da rigakafin rigakafi kuma a fara maganin diphtheria antitoxin lokacin da ta nuna alamu.

 

 

5. Duk ma’aikatan kiwon lafiya (likitoci, ma’aikatan jinya, masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, ma’aikatan tallafi, da sauransu) waɗanda ke da yawan kamuwa da cutar diphtheria yakamata a yi musu allurar rigakafin diphtheria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...