An yi bikin saukar dalibai 16 a Madarasatus Salafiyya Littahafizil Qur’an dake R/Lemo

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Makarantar Madarasatus salafiyya littahafizil Qur’an dake unguwar Rijiyar lemo ta yaye dalibai guda 16 da suka sauke al-Qur’ani mai girma.

 

Yayin bikin saukar Justice R. A Sadeeq ya bukaci daliban da suka sauke da su Kara Mai da hankali wajen yin tilawar karatun da aka koya musu, domin hakan ne zai sa karatun ya zauna sosai a kwakwalwarsu.

 

Talla

Ya kuma bukace su da su sake daura damar cigaba da neman Ilimin sauran fannonin addinin musulunci, domin da shi ne zasu san Allah da kuma yadda zasu bauta masa tare da sannnin yadda zasu yi mu’amala da al’umma.

 

  • ” Sauran dalibai Ina kira gareku da ku himmatu wajen ganin kuma kun sauke al-Qur’ani mai girma, Kuma Ina yabawa Iyayen wadannan dalibai saboda yadda suka jajirce wajen Kun yi karatu Mai nagarta, Kuma ma malamai dole mu yabawa kokarin ku Kuma Allah ne kadai zai biya ku.” Inji Justice R.A Sadeeq

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Da yake nasa jawabin Dagacin yan mata Alhaji Auwalu Abdulkarim ya hori sauran iyayen yara da su kara kaimu wajen ganin sun tura ‘ya’yansu makarantun Islamiyya domin su sami Ilimin yadda zasu bautawa Allah subhanallahu wata’ala.

 

Ya yabawa daliban saboda yadda suka jajirce har sai da suka sauke al-Qur’ani, sannan ya yabawa malaman makarantar bisa kokarin da sukai wajen ganin sun koyar da al-Qur’ani ga dalibai da sauran fannonin addinin musuluncin.

 

Shi kuwa Shugaban makarantar Malam Umar godiya yayi ga mahalarta taron bisa yadda suka amsa gayyatar su, sannan ya godewa iyayen daliban makarantar Saboda hadin kai da suke baiwa makarantar wajen ciyar da makarantar gaba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...