Buhari ya Amince Nigeria ta yi Sulhu da Twitter

Date:

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na tattaunawa da Kamfanin ta Twitter kan dakatar da ayyukan ta da aka yi kwanan nan a Najeriya.


 Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da Tattaunawar don ganin an cimma matsaya tsakanin Gwamnatin Tarayya da kamfanin na Twitter.


 Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda zai shugabanci tawagar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
 A cewar sanarwar, tawagar Gwamnatin Tarayya ta hada da Babban Lauyan Gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, sai Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, da Ministan Harkokin kasashen Waje, da Ministan Ayyuka da Gidaje,  Karamin Ministan Kwadago sauran hukumomin gwamnati da suke da alaka da Harkar. 


Ida za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa gwamnatin tarayya a kwanakin baya ta dakatar da aiyukan Twitter a Nigeria Sakamakon goge rubutun da Shugaban Kasa Muhd Buhari yayi akan Tsagerun Kudu Maso gabas Masu fafutukar Kafa Kasar Biafra.

145 COMMENTS

  1. Усик — Джошуа. Букмекери зробили прогноз на бій. Редкач аргументував такий сміливий прогноз тим, що попередні олімпійські чемпіони, яких побив Джошуа, були на заході кар’єри, тоді як Усик Энтони Джошуа Александр Усик Рен ТВ Усик показал рекордный вес перед боем с Джошуа (видео

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...