Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar masu sana’ar kayan gwari ta jihar kano, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta jiha da su kawowa fannin harkokin noma daukin gaggawa domin kara bunkasa kasuwancinsu.
Shugaban kungiyar Malam Hamisu Abubakar ne ya bukaci hakan lokacin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 a ofishin sa.
Hamisu Abubakar yace, akwai bukatar gwamnati ta kawo wasu sabbin tsare-tsaren da za su agazawa manoma da masu sana’ar kayan gwari don inganta kasuwancin su da kuma rayuwar su.
” Ya kamata Muna a rika sa mu cikin wadanda ake tallafawa da jari ko Kuma sabbin dabarun yadda zamu inganta harkokin mu, kamar yadda ake yiwa sauran masu sana’o’i”.
Yace kungiyar masu kayan gwari, kungiyace da take taka rawar gani a cikin al’umma, Amma gwamnatin tarayya data jiha suna nuna mana wariya wadda bamu san dalili ba.

Shugaban ya yabawa Gwamnatin jihar kano, bisa kokarinta na ganin ta inganta rayuwar al’umma da kawo managartan tsare-tsare domin ciyar da jihar kano gaba, musamman ta fannin harkokin yaki da shan miyagun kwayoyi da dai sauransu.
” kungiyar masu sana’ar kayan gwari dake karkashin gadar masallacin fagge da kasuwar kofar wambai, ta himmatu wajen dakile masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ko batagarin al’umma dake cikinsu har ma dana waje da za su zo domin su fake a cikin su”.
Kungiyar tana iya kokarinta wajen samarwa matasa sana’o’in dogaro da kai duk kankantarsu, kasancewar sana’arsu ta masu karamin karfice dake bukatar gwamnati ta kawo musu dauki da agaji da tallafin da za su bunkasa kasuwancinsu .
Hamisu Abubakar yace, kungiyar masu sana’ar kayan gwari ta jihar kano, ta dade tana tattarawa Gmgwamnatin jiha da tarayya kudaden haraji, amma har yanzu ba, a kawo mata wani dauki na taimako daga gwamnati ba,yace har yanzu suna sanya ido domin ganin ko wanene zai baiwa kungiyar tallafi ba.
Shugaban ya kuma yi kira ga ‘ya’yan kungiyar da su ci gaba da baiwa shugabancin kungiyar cikakken goyan baya da hadin kan daya dace, domin samun bijiro da managartan tsare tsare da za su bunkasa kasuwancinsu da rayuwarsu .