Wata babbar mota ta hallaka jami’an Road Safety 2

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Wani direban babbar mota ya kashe jami’an Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta Najeriya biyu a kan babbar hanyar Aba da ke kudancin ƙasar.

 

A wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sannun babban jami’in wayar da kan jama’a na hukumar Bisi Kazeem, ya ce muƙaddashin babban shugaban Hukumar Dauda Ali Biu, ya bayyana damuwarsa game da kashe jami’an hukumar biyu, tare da alkawarta gurfanar da waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar jami’an a gaban kotu domin su fuskanci hukunci .

 

Talla

Sanarwa ta ce Mista Biu ya yi Allah wadai da wannan lamari da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an hukumar waɗanda ke bakin aikinsu, sakamakon abin da ya kira ‘aikin direbobi masu tukin ganganci waɗanda ke ci gaba da karya dokar tuƙi’

An sace kayan fitar angwanci na wani ango a Kano

Lamarin ya faru ne sakamakon ƙoƙarin kauce wa rami da direban babbar motar ya yi, yayin da yake tsaka da gudu a kan hanyar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

 

Jami’an hukumar FRSC dai sun daɗe suna zargin direbobin ƙasar da tukin ganganci tare da gudun wuce kima a kan titunan ƙasar, lamarin da hukumar ke cewa shi ne musabbabin mafi yawancin haduran da ke aukuwa a kan titunan ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki – Ministan lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta...

Sarkin Hausawan Arewa, Amb. Balarabe Tatari, Ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Buhari da Dantata

Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Alhaji Balarabe...

INEC ta sanya ranar fara rijistar masu zabe a Nigeria

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan...