Satar Waya: Kotu ta yankewa Wasu Matasa 6 Hukunci

Date:

Daga Umar Ibrahim Sani Mainagge


Babbar kotun shari’ar musulunci Mai lamba daya karkashin jagorancin Mai Shari’a Malam Ibrahim sarki Yola ta Kama Wasu Matasa guda 6 da laifin Satar wayoyin jama’a.

Jami’an ‘yan sanda ne dai dake ofishin Yan Sanda na kwalli suka gurfanar da wasu Matasan a gaban kotun, Matasan su 6 sun hadar da:
1- Umar Ahmad
2-Abba sani
3-Abubakar yusif
4-Ahmad mustapha
5-Aliyu Bashir da Kuma Ahmad Musa

An dai kama matasan ne a mabanbanta unguwanni cikin birnin kano tare da zabga-zabgan wukake da Kuma wayoyin hannu masu tsadar gaske har guda takwas (8) .

Gaba daya matasan dai sun amsa laifinsu bayanda lauyan gwamnati ya karanta musu kunshin tuhumar da ake musu.

Bayanda ya saurari bangarorin biyu (2) alkalin kotun Mal Ibrahim Sarki Yola ya yanke musu hukuncin daurin kwana dari da tamanin a gidan gyaran hali da tarbiyya aka umarci Dan wanka ya wankesu da bulala ashirin (20) ga kowannensu tare da damkasu a hannun jami’an gidan hali na kotun, tiri-tiri sai munyi unguwar zangina da abokin aikinsa Ali Ado Badawa domin su wuce dasu zuwa wancan gida.

Bayanda fitowa daga kotun muka ji daya daga cikin Wanda ya fada komar wadannan matasa,Inda yace Matasan sun nuna Masa Makami ne kafin su karbi wayarsa.

Wakilin Kadaura24 yaso jinta Bakin bangaren matasan da aka yankewa hukuncink sai dai sunyi gum da bakinsu.

14 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...