Kwankwaso ba zai halarci taron tattaunawa da yan takarar shugaban kasa ba

Date:

Dan takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam’iyyar NNPP, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai halarci taron tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa da hadakar kungiyoyin Arewacin kasar suka shirya, saboda zarginsu goyon bayan wani dan takara.

Wasu hadakar kungiyoyin arewacin kasar da suka hadar da kungiyar Arewa Consultative Forum, da kungiyar Arewa House, da gidauniyar Sir Ahmadu Bello, da kungiyar Northern Elders Forum da kuma kungiyar Arewa Research and Development Project ne suka shirya taron tattaunawar tsakanin ‘yan takarar shugabancin kasar.

Talla

A wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar Abdulmumin Jibrin kofa, ya sanya wa hannu, ya kuma wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce, ya bayyana cewa Kwankwaso ya riga ya shirya yakin neman zabe a ranar da aka tsara zai yi jawabi a taron.

Sannan kuma sanarwar ta yi zargin cewa sun sami sahihin labarin da ke cewa wasu daga cikin masu shirya tattaunawar na da wata manufa, sannan kuma za su yi amfani da taron ne wajen nuna goyon baya ga wani dan takara

An dai tsara cewa Kwankwaso zai yi jawabi a gaban taron tattaunawar ranar Litinin, tare da dan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour, a yayin da tuni Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya riga ya gabatar da nasa jawabin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...