Sarkin Kano zai Halarci Gagarumin Bikin Gargajiya na Dawaki a Kasar Morocco

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya bar Najeriya zuwa kasar Marocco domin halartar bikin dawaki na kasa da kasa karo na 13 a birnin El-Jadida da ke gabar teku tsakanin 18 ga Oktoba, 2022 zuwa 22 ga Oktoba.

 

Sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace Masu shirya wannan biki ne suka gayyaci Sarkin na Kano a matsayin babban bako a lokacin bikin.

Talla

Bikin gargajiyan na hawan dawakin yana amfani da fa’idodi masu yawa wadanda suka hadar da cigaban bunkasar harkar Noma, haɓakawa da adana al’adun gargajiya, muhalli, wasanni a matsayin tushen nishaɗi wanda ke haifar da alaƙar zamantakewa mai ƙarfi.

 

Buga da kari bikin na wannan shekara zai ƙunshi sabbin abubuwa da dama tare da nishaɗi da al’adu da fasaha da wasanni da gasar wasan dawaki tare da halartar ƙasashen Afirka da yawa.

 

Talla

Tuni dai wata tawaga daga Kano tayi tattaki zuwa Masarautar ta Marocco domin halartar bukukuwan da gasa a yayin bikin.

 

NNPP ta yi kira da a hukunta Ciyaman ɗin APC da aka kama da katunan zaɓe 300 a Kano

Alhaji Aminu Ado Bayero CFR yana tare da Alh. Ahmad Ado Bayero Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Amb. Ahmed Umar OON Dan Malikin Kano da Mal. Isa Bayero, da sauran ma’aikatan ta Kano.

 

Ana sa ran dai Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai dawo gida Najeriya a ranar Lahadi 23 ga Oktoba, 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...