Daga Kabiru Muhammad Get so
Tsohuwar ‘yar takarar mataimakiyar Shugaban kasa a jam’iyyar YPP Hajiya Umma Getso ta bayyana cewar yanzu haka al’ummar kasar nan na cikin wani irin hali tare da fatan samun sabuwar Gwamnati Da zata fi wannan Gwamnati da muke cikin ta Buhari.
Umma Getso ta bayyana haka ne lokacin da take ganawa da manema labarai a dai dai lokacin da ake murnar tunawa da ranar samun ‘yancin kai.
Tace babu wata riba da aka samu a wannan Gwamnati musamman idan akayi la’akari da matsalar tsaro,fatara da karuwar rashin aikin yi ga matasa.
Umma Getso wacce take daya daga cikin mata ‘yan Gwagwarmaya masu fafutukar kawo sauyi a kasarnan, tace duk da yanzu ta fita daga ‘yamiyyar da tayi takara a baya babu shakka zata yi duk Mai yiwuwa wajen wayar da kan Al’umma musamman mata domin zaban Jam’iyyar da ta dace da kawo sauyi a kasarnan.
KaZalika tayi kira ga mata da matasa da kada su bari ayi amfani dasu wajen tada zaune tsaye a wajen yakin neman zabe.
Maimakon hakan kamata yayi subi matakai daban daban wajen zabar wadanda zasu taimakesu da kuma dawo da kasar bisa kyakkyawan tsarin da zai canda yanayin kasarmu Nigeria.
Ta kara ta cewar abun takaicine ace Nigeria tana da shekaru 62 amma har yanzu Ana kallon kamar har gara ma lokacin kasar tana hannun turawa.