Makarantar firamare ta Jangaru dake Ungoggo tana bukatar kulawar gwamnati don inganta ilimi a yankin – Kungiyar tsofaffin dalibai

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar
Shugaban kungiyar tsofaffin daliban makarantar firamare ta Jangaru dake Kunture a karamar hukumar ungoggo a jihar kano Abubakar  jibril yayi kira ga gwamnatun jihar kano da masu rike da madafun iko a karamar hukumar dasu taimakwa makarantar jangaru da kayan koyo da koyarwa domin inganta ilimin yaran dake yankin.
Abubakar Jibril ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakiliyar kadaura24 a kano.
Yace a bayan kunguyarsu ce take taimakawa makarantar da kayan karatu da kuma abun zaman dalibai da dai sauransu , amma yanzu yace lamarin yafi karfin su dole sai gwamnati ta shigo don tallafawa ilimin daliban makarantar.
Talla
“Yanzu haka wannan makarantar firamare ta jangaru tana bukatar samun sabbin ajujuwa, sannan tana bukatar a gyara na baya da ake dasu, saboda mafi yawa daga cikinsu idan akai ruwan sama basa shiguwa saboda yadda ruwa yake zuba a cikinsu”. Inji shugaban kungiyar
Mun sani gwamnati tana kokari wajen inganta ilimi a jihar kano, kuma dole a yaba mata saboda irin kokarin da take yi hakan tasa muka ga dacewa yin kira da babbar murya da a kawowa makartarmu daukin gaggawa ko dan kannenu da ‘yayanmu suma su shaida kokarin da ake na inganta ilimi a kano.
Talla
” Wannan makaranta ta Jangaru firamare da ke unguwar kuntire karamar hukumar Ungoggo tana bukatar kayan karatu bandakuna office din malamai na maza dana mata  bencinan yara da dai  sauransu”. Inji Abubakar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...