Daga Rahama Umar kwaru
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace masarautar Kano tana bayar da gagarumar gudunmawa wajen kula da lafiyar al’ummar jihar kano.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen taron makon lafiya na shekara ta 2022 da Ma’aikatar lafiya ke shiryawa duk shekara kuma aka gudanar a dakin taro na Coronation dake gidan Gwamnatin jihar Kano.

Cikin sanarwar da sakataren yada labaran masarautar kano Abubakar Balarabe kofar na’isa ya aikowa kadaura24 yace Alhaji Aminu Ado Bayero yace Masarautar ta Kano tana wayar dakan al’umma domin karbar aikace-aikacen kiwon lafiya musamman rigakafin yau da kullum da rigakafin cutar Covid 19 da yaki da cutar shan Inna, Inda yace hakan yasa jihar Kano da kasa baki daya aka sami shaidar kawar da wannan cuta.

Ya nuna farin cikinsa bisa gudanar da taron tare da nasarorin da Gwamnatin Kano ta samu a bangaren lafiya karkashin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam.
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi bayanin cewa kamar yadda yagani Gwamnatin jihar Kano tayi matukar kokari musamman idan akayi la’akari da yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziki a duniya baki daya.
Ya taya Gwamnan kano murnar samun nasarori a fannin lafiya tareda godewa ubangiji bisa ni’imar shugabanci nagari da ya bayar inda yayi fatan samun jagorancin Allah madaukakin Sarki.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi fatan taron zai zama wani dandali na kara zage damtse domin cigaba da irin wadannan muhimman ayyuka da kuma zaburar da ma’aikata da al’uma wajen tallafawa shirye shiryen kiwon lafiya.