Daga Babangida Kano
Ambayyana tsare tsare da kyakkyawan manufofi ne suka sa dantakarar gwamnan jihar kano karkashin inuwar jam’iyyar ADP Hon Sha’aban Sharada matsayin kashin bayan komawarsa jam’iyyar.
Batun hakan nazuwane daga bakin babban Sakataren tsare tsare na jam’iyyar na jihar kano Kuma jigo a matakin kasa na jam’iyyar Ambassador Tasi’u Abdulrahman awata zantawa da kadaura24.
Sakataren yaci gaba da cewa kasancewar Dantakarar yanada matsaloli da jam’iyya APC da ya Kai su zuwa kotu Kuma ba warwareba yabashi damar komawa ADP, sukuma suka karbe shi hannu biyu-biyu Kuma suka bashi takara bisa cancantar sa.
Ambasada Tasi’u,yakara dacewa su a jam’iyyar ADP suna da dokokin da mutum bazai samu shigaba har sai ya amince dasu tukunna yasamu shiga,dan kaucema matsalolin daka iya faruwa.
Sannan shugaban kwamitin tantance Yan takarar na ADP matakin kasa da jihohin Kano da Jigawa,ya bayyana batun cewa yin abu babu wasu daga cikin masu alhaki yake kawo matsala ga jam’iyya kowacece,dan haka sukan yi magana da murya daya tun daga matakin kasa har jiha da kananan hukumomi dan samun matsaya guda kafin aiwatarwa.
Sannan yace tsarin jam’iyyar ADP shine ayi dai-dai,kuma shine yabasu damar shigar ta,tun tsawon lokaci dan haka suke kallon tsarin ta na farar hula sabanin sauran jam’iyyun wasu gyauron Sodojin ne dan haka dole asamu bambanci atafiyar mu dasu ta fuskar tsari da manufofi.
Kazalika yayi batun manufar jam’iyyar ADP na ba matasa dama Kamar yadda marigayi Bashir Tofa yadora su akai na cewa su ba matasa dama, saboda matasa na san suyi siyasa amma kasancewar babu jagororin daza su yi ma su jagoranci yasa suka dora matasan kan wannan turba.
Wasu daga cikin makasudin da yasa suka samar da jam’iyyar a Kan turbar jagoran cin su batun gyaran matsalar ilimi, Lafiya da Kuma matsalolin ruwan sha ga hanyoyi da suka lalace a jihar kano,abin sai wanda yagani.
Ambasada Tasi’u,ya bukaci al’ummar jihar kano dama kasa baki daya da su yi karatun tanatsu dan shugabanin da zasu kawo masu cigaba, yaka kuma ce ADP a shirye ta ke dan kawo dauki daga yanayin da shugabanin yanzu suke mulkin juya hali ga talakawa.