Daga Abdulrashid Habib Tukuntawa
Al’ummar garin Jar kuka layin Mai allo daya hade kananan hukumomin Gezawa Nasarawa da Kumbotso sun koka saboda lalacewar hanyar shiga garin, Inda suka ce suna Shan wahala sosai kafin shiga ko fita daga garin.
Wani jagoran cikin mazauna garin mai suna Kabiru Ya’u shi ne ya bayyana hakan a amadadin al’ummar gari yayi ganawarsa da wakilin Kadaura24 a kano.
” Yanzu haka idan an fara girbin amfanin gona bamu San yadda zamu yi ba, wajen fito da su zuwa kasuwannin ba, don haka idan Allah bai takaita ba zamu yi asara mai yawa a bana, Amma dai Muna fatan Allah ya kiyaye”. Inji Kabiru Ya’u
Yace Mutane garin sukan shiga halin Mawuyacin hali sakamakon Rashin kyawun hanyar saboda hanyar tayi lalacewar da da kashi garin a mota a adaidaita sahu gara ka shiga da kafa, saboda ran ka sai ya baci.
” Yanzu haka mata Masu juna biyu sukan haihu a hanya ko su jigata kafin akai su asibitin duk a dalilin lalacewa hanyar garinmu na jar kuka layin mai allo, motocin da suka lalace a hanyar kuwa Allah ne kadai yasan yawansu”. Inji shi
” Kamar yadda kuka gani wanann hanya tamu bata shiguwa idan akai ruwan sama Kuma mu kwashe lokuta masu yawa Muna cikin Wannan yanayi, idan akai ruwan sama wallahi Masu baburan adaidaita sahu basa yadda su shigo cikin garin nan, saboda sun ce wai baburan su lalacewa suke”. A cewar Kabiru Ya’u
Kabiru Ya’u ya yi kira ga Masu ruwa da tsaki da hanyar garin nasu da su kai musu daukin gaggawa don fitar da mutane masu tarin yawa daga cin mawuyacin halin da suke tsintar kansu.