Daga Sani Abdulrazak Darma
An bukaci Direbobi da masu kasa kaya akan titin IBB zuwa kasuwar Kofar wambai dasu kiyaye dokokin da hukumomi suka shinfida, domin kaucewa gamuwa da haddura.
Shugaban Karota dake lura da masallacin Idi , IBB zuwa kofar wambai, da kasuwar kwari Jamilu Dambatta ne ya bayyana hakan yayin ziyara ta musamman da suka kaiwa Sabon DPO na Kofar Wambai.
Jamilu Dambatta yace sun kaiwa DPOn ziyarar ne domin kula alakar aiki tare da kawo cigaban aikin su, da kuma kawar da duk wata matsala da ake fuskanta.
Kazalika Shugaban Karota na Masallacin Idi OC Jamilu Dambatta yaja hankalin ‘yan kasuwar masu kasa kaya akan hanya dasu daina, haka zalika, suma direbobi dasu daina toshe hanyar da Jama’a suke shigewa.
Anasa Jawabin Saban DPOn Kofar wambai Police Statation Muhd Ya godewa ‘yan karotar da suka kai masa ziyarar, inda yaci Alwashin yin aiki tare dasu.
Ya kuma bukaci ‘yan Sandan dake aiki a sashin kofar wambai su zamo masu gaskiya da Adalci, batare da cin Zarafin Kowa ba.
Wakilin kadaura24 ya rawaito mana cewa ‘yan Karotar dake karkashin kulawar Jamilu Dambatta maza da mata ne suka halarci ziyarar a Ofishin Baturen ‘yan Sandan Dake Kofar Wambai.
Yin aiki tukuru da kwatanta gaskiya shi ne abinda yake daga darajar mutum a cikin aikin sa.