Daga Aminu Garba Indabawa
Tsohon dan takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar PDP Ibrahim Al-amin Little yace tunda Malam Ibrahim Shekarau ya shigo jam’iyyar PDP babu makawa shi ne Jagoran jam’iyyar a Kano.
Ibrahim little ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a Kano cikinsu har da wakilin Kadaura24.
Yace kai tsaye Malam Shekarau shi zai zama Jagoran jam’iyyar tun da ya shiga jam’iyyar ta PDP da kujerar Sanata kamar yadda Kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bayyana.
” Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyarmu ta PDP ya bayyana cewa idan da gwamna Mai ci a jihar shi ne Jagoran jam’iyyar in Kuma babu tsohon gwamnan sai ya riƙe jagorancin, ko Kuma wanda ya rike Mukamin Minista ko Sanata Mai ci, shi Kuma Malam Ibrahim Shekarau shi ne Sanatan Kano ta tsakiya Kuma ga shi tsohon gwamnan don haka kai tsaye shi ne Jagoran jam’iyyar PDP na jihar kano ” inji Ibrahim little
Ibrahim Al-amin Little wanda yake jagorantar wasu kungiyoyi na yada manufofin Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku ya yiwa Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayan sa Barka da shiga jam’iyyar ta PDP, Inda ya bada tabbacin shigar Shekarau PDP zai Kara mata karsashi sosai a kano da kasa baki daya.
Idan za’a iya tunawa a shekara ta 2014 da Malam Shekarau ya shiga jam’iyyar ya iske Amb. Aminu wali a matsayin Jagoran jam’iyyar Saboda yana rike da Mukamin Minista daga bisani shi ma aka nada shi a mukamin Minista hakan tasa suka haɗa kai suka jagoranci jam’iyyar da Malam Shekarau da Amb. Aminu wali.
Amma yanzu ana ganin ba lallai a sami wata matsala ba game da jagorancin jam’iyyar Saboda yanzu Malam Ibrahim Shekarau shi kadai ne yake rike da Mukami a jam’iyyar PDP ta jihar kano.