Hukumar Karota ta Kama Wata Mota Makare da Giya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar Karota ta Jihar Kano tayi nasarar cafke wata tirela makare da barasa, a kan titin Bello Dandago dake kwaryar birnin Kano.

 

Jami’an karotan sun kama motar ne da misalin karfe 2:30 na daren Larabar da ta gabata, a ƙoƙarin su na shiga cikin Sabon Garin Kano.

 

Jami’an Hukumar ne suka sami nasarar cafke motar a lokacin da suka buƙaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abinda ya ɗakko ta Way bill, inda ya bayyana musu cewa Kwali ya ɗakko.

Rigakafi : Gidauniyar Dangote, Gwamnatin Kano, UNICEF, Billgate sun sanya hannu kan wata yarjejeniya

 

Bayan da jami’an suka matsa bincike sai suka tabbatar da Giya ce a cikin babbar motar.

 

Shugaban Hukumar KAROTA Hon Baffa Babba Ɗan’agundi, ya bayyana cewa Hukumar KAROTA ba za ta gajiya ba wajen kama duk wani nau’in kayan da aka ci garo da su, wanda dokar jihar Kano bata amince a shigo da su ba.

Inganta Ilimi: Kawu Sumaila ya Baiwa Wata Yarinya Gurbin Karatu a Jami’arsa ya Al-Istigama

 

Ya ƙara da cewa za a ƙara baza jami’an KAROTA musamman kan manyan titinan jihar nan, domin ganin an daƙile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano ta haramta.

 

Ƙasa da mako guda hukumar ta cafke manyan motocin Tirela maƙare da Giya wadanda adadinta ya kai fiye da Kwalba dubu arba’in (40) da kuɗinta ya haura naira miliyan arba’in 40.

 

Da zarar an kammala bincike za a miƙa Giyar ga Hukumar Hizba ta jihar kano domin ɗaukar mataki na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...