Daga Rabi’u Usman
Rundunar Vigilantee ta Jihar Kano ta ce ta Samu Nasarar Dakume Wasu Mutane 5 da ake Zargin Barayin Shanu Ko Kuma Masu Garkuwa da Mutane ne a Dajin Gurbi Cikin Karamar Hukumar Gwarzo da Suka Koro Shanu guda Dari Biyu (200), da Kuma Tumakai Sama da Dari (100) daga Kasar Nijar Zuwa Nan Kano.
Bayanin Hakan ya Fito ne ta Bakin Babban Kwamandan Rundunar Muhammad Kabir Alhaji yayin da yake Ganawa da Manema Labarai a Wannan Rana ta Juma’a .
Mk Alhaji yana mai Cewar, Sun Samu nasar Kama Mutanen ne bisa bayanen Sirri da suka samu, hakan ta Sanya Suka Baza Komar Su Domin Ganin Sun Kama Wadannan Mutane da aka Basu Bayani a Kansu.
Ya Kara da cewa, Basu Samu Damar Kama Su ba Sai da Suka Bisu har Zuwa Karamar Hukumar Karaye Sannan Allah ya Basu Ikon Kama Wadannan Mutanen da Suka Koro Shanu daga Jumhuriyar Nijar.
A Karshe dai Kwamandan yayi Kira ga Al’umma dasu Kasance Masu Taimakawa Jami’an Rundunar Vigilantee da Kayan Aiki harma da Basu Bayanan Sirri da Zarar Sunga Motsin Abin da Basu Amince da Shi ba.
Mk Alhaji Yace zasu Mikawa Yan Sanda Mutanen domin gudanar da bincike akan su tare Kuma da gurfanar dasu a gaban Kotu.