Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan batun sauya wa ƙasar suna zuwa United African Republic (UAR) da yake ta jan hankalin ƴan ƙasar a yau.
Fadar shugaban Najeriya ta nesanta kanta daga wannan lamari, inda ta ce ba ita ta gabatar da ƙudurin sauya sunan ƙasar ba.
Mai taimaka wa shugaban ƙasar na musamman kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa a shafin Tuwita cewa Shugaba Buhari ba shi da hannu a batun sauya sunan.
“Ba gwamnatin Najeriya ko Shugaba Buhari ne suka miƙa buƙatar sauya sunan ba, mutane ne ƴan ƙasa suka yi hakan a wajen jin ra’ayoyin jama’a.
“Amma tuni wasu mutane suka ɗauki abin suka ɗora a ka suna zargin shugaban ƙsa wanda ba shi da hannu sam a ciki,” a cewar saƙon na Bashir.