Muqabala : Mai aljana yace Duk abin Daya fada Karya ne, Bai Auri aljana ba

Date:


Daga Umar Usman Sani Mainagge


Gwamnatin jihar Kano ta titsiye Mutuminan dan Kofar Na’isa da yayi da’awar ya auri aljanna har sun haifi ‘ya’ya da ita.


A gudanar da titsiyen ne a ofishin Kwamishinan ma’aikatar addini ta jihar Kano Dr. Tahar Baba Impossible dake gidan murtala a Nan birnin Kano.


 Tun a baya dai Ahmad Ali dake unguwar k/Na’isa Wanda akafi sani da Mai aljana yayi shuhurane da hulda da aljana da bada magungunan gargajiya, harma ya shaidawa kafafan yada labarai dana sada zumunta cewar wai ya auri aljana mai suna ummusibyan harma sun haifi ‘ya’ya tare.


Wancan furuci na Mai aljana ya baiwa Mutane mamaki sosai Saboda yadda yace mahaifin aljanar ne ya aura masa ita Saboda Dama shi a wajen aljanu ya girma sun Saba da juna sosoi.
To Bayan wancan furuci al’umma sun Yi ta kalubalantar Mai aljana ,hakan tasa gwamnatin Jihar Kano magantuwa Saboda yadda al’ummar suka Dauki Maganar da Kuma gujin kada Shi Mai aljanna ya jefa Mutane Cikin bata. Shi ne yasa Gwamnatin ta shirya Wannan Zama a Wannan Rana.


To sai dai a0 Mai aljana yayi karo da goshi jirgi domin yace ya janye duk kalamansa na baya tare da zubda makamansa bayan daya Sha matsa irinta Mai a gaban kwamashinan addinai.
 Bayan janye bayanan da yayi a baya Mai aljana ya shaidawa Duniya cewa ya saki Matarsa Amma aljanar har saki uku a gaban al’umma a ofishin kwamashinan Dr. Tahar Baba impossible.


Wakilin Kadaura24 ya tambayi Mai aljana cewa a Bayan mun ji matarka Mutum tace har raba Kwana suke da amaryarka aljana” Mai aljana sai ya kada Baki yace ” kawai dai ta Fadi hakan ne domin ta Kare Mana Abincin mu, Amma Karya take Yi.

 A Jawabinsa Kwamishinan harkokin addini na Kano Dr Tahir Baba Impossible yace sun shirya Titsiyen ne domin Gudun kada al’umma su fada Haka ta sanadiyyar kalaman Mai aljanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...