Jirgin Ruwa ya Nutse da Sama da Mutane 100 a Kebbi

Date:

Daga Umar Sani K/Na’isa

Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu bayan wani jirgin ruwan da suke tafiya a cikinsa ya nutse a wani kogi da ke jihar Kebbi .

Lamarin ya faru ne yau Laraba da misali karfe 10 na safe, kuma bayanan da ke fitowa daga yankin na cewa kawo yanzu ana ƙoƙarin ceto waɗanda ya rutsa da su.

Bayanai dai na cewa jirgin ya taso ne daga Lokon Minna a jihar Neja zuwa garin Wara jihar na Kebbi dauke da mutane sama ga 160 da suka hada da maza da mata da ƙananan yara.

Amma sai jirgin ya rabe gida biyu ya kuma nutse tare da dukkan mutanen da ke cikinsa ana dab da isa garin na Wara

Shaidu dai sun ce baya ga ɗauko ninkin adadin mutanen da ya kamata ya ɗauka, an kuma saka masa buhunan yashi da ake haƙowa daga mahaƙar zinare.

Shugaban karamar Hukumar Ngaski ta jihar Kebbi Abdullahi Buhari Warah wanda ya ziyarci wajen da lamarin ya faru don ganin yadda ake aikin ceton ya ce lamarin akwai ban tausayi.

“A haƙiƙanin gaskiya mun je babban bakin kogin da ke garin Wara inda akwai mutanen da ke kuka idan suka fito daga cikin ruwan. Akwai mutum sama da 160 a cikin jirgin.

“Wani da ya fito daga cikin jirgin ya ce babu ceto kuma akwai ƙananan yara da dama da suka nutse a tekun don babu mai cetonsu.

“Akwai ma wani dan jihar Zamfara da ya ce min akwai wasu yan gida daya su takwas kuma duk sun niutse.

Hatsarin jirgin ruwa a Kabbi
Hatsarin jirgin ruwa a Kabbi

Ya ce zuwa yanzu ba za a iya tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, “akwai mutum 22 da aka ceto daga wasu bangarori na sassan wasu ƙauyuka da ke kusa kogin an kuma kai su asibitin Wara

“Sannan gawa ɗaya kawai aka samo zuwa yanzu ta wata yarinya.

Hon. Abdullahi Buhari ya ƙara da cewa a ƙa’ida jirgin yana ɗaukar mutum 65 ne zuwa 80 amma sai ga shi ya lodi mutum 160.

Sai dai Honorobul ya ce ba laifin hukumomin Kebbi ba ne ta wajen yin lodin da ya fi ƙarfin jirgin da kuma ƙin sa rigar da ke hana nutsewa.

Daga cikin fasinjojin jirgin dai akwai wadanda ke suka sa rigar kariya daga nutsewa amma kuma sai suka cire suka ba wasu saboda a cewarsu akwai zafi.

wani wanda ya tsallake rijiya da baya Mai Suna Umar Usman yace lamarin Allah ne kawai yasa ya faru Saboda Babu wani Dutse ko Wani abun da Zai iya Sanyawa jirgin ya karye.

“yanzu Haka Mutane da dama ne suke Cikin Ruwan Cikin Mutane Sama da dari mu biyu ne zuwa uku Mike Asibiti sai Wani mutum da aka wuce dashi jega”. Inji Umar Usman

Hadari irin wannan dai ba bakon abu bane a wannan yankin na jihar Kebbi kuma yawanci akan danganta su ga daukar mutane fiye da kima da kuma yadda jiragen ke cin karon da kututtutan itatuwan ke tsirowa a cikin kogin.

Ko a wata Satumban bara hadarin irin wannan a jihar ta Kebbi ya yi sanadin mutuwar mutum takwas

215 COMMENTS

  1. Джошуа: Усик вміє боксувати, він серйозний претендент – Бокс Энтони Джошуа Александр Усик смотреть онлайн Він переконаний, що Олександр Усик розпочне бій активніше, а чемпіон буде спершу вичікувати. Але Вайт наполягає, що у проміжку між 5-м та 7-м раундами Джошуа переможе Усика нокаутом.

  2. Екс-суперник Усика вірить в українця в бою з Джошуа — МЕТА AnthonyJoshua Новые видео Усик Джошуа на сайте Zvidos.ru. Смотрите бесплатно ????ВЗВЕШИВАНИЕ !?АЛЕКСАНДР УСИК ЭНТОНИ ДЖОШУА. ЖДЁМ БОЙ. БОЛЕЕМ ЗА САНЮ, Взвешивание УСИК vs ДЖОШУА! РЕКОРДНЫЙ ВЕС, Джошуа – Усик Прогноз на бой от экс

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...