Jamia’ar Wudil za ta hukunta mazan da suka yi wa ɗaliba ihun saka abaya

Date:

Mahukuntan jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil dake nan Kano ta ce za ta ɗauki “mummunan mataki” kan ɗaliban da suka ci zarafin wata ɗaliba saboda ta saka rigar abaya.

Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a jiya Talata, shugaban sashen harkokin ɗalibai ya nemi afuwar ɗalibar sannan ya buƙaci ta shigar da ƙara a hukumance domin neman haƙƙinta.

A jiya Talata ne aka ga wasu matasa na jan abaya da wata ɗaliba ta saka tare da yi mata ihu cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta a wani wuri da aka ce cikin jami’ar ne ta Wudil.

“Hukumar Kano University of Science and Technology Wudil ta samu ƙorafe-ƙorafe daga shafukan zumunta game da wata ɗaliba da ɗalibai maza suka ci zarafinta saboda ta saka abaya,” a cewar sanarwar.

“Ni shugaban sashen harkokin ɗalibai zan ɗauki mummunan mataki a kan wannan lamari. Ɗalibai su sani cewa su ba hukuma ba ce da za su ci zarafi ko ɗaukar mataki kan wani, sai dai kawai su kai rahoto wurin jami’an tsaro.”

Sanarwar ta ce abaya ba ta saɓa wa dokar saka tufafi ta jami’ar ba, “saboda haka ɗalibar ba ta karya wata doka ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...