Ganduje ne ya baiwa NLC kudi sukai Zanga-zanga a Kaduna-El-Rufa’i

Date:

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El Rufa’i ya zargi gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da daukar nauyin kungiyar kwadago NLC don Yi Masa Yajin aiki da Zanga-zanga.


Cikin wani faifan audio dake yawo a kafafen sada Zumunta an jiyo Gwamna Nasir El Rufa’i na zargin da hadin bakin gwamnan Kano akan Waccen tirjiya daya fuskanta daga gamayyar kungiyoyin kwadago.

“Gwamnan Kano Ganduje ne ya baiwa Yan Kungiyar Kwadago kudi domin su yi Zanga-zanga a jihar Kaduna”Inji El-Rufa’i Cikin harshen Turanci


Gwamnatin jihar Kano dai batace uffan ba kan wannan zargi, sai dai masu lura da al’amura na ganin cewa gwamnan na Kaduna ya girbi abinda ya shuka ne na korar ma’aikatan jihar tare da kin yadda asamu maslaha da kungiyoyin na kwadago.


A makon daya karene kungiyar kwadago ta NLC da sauran takwarorinta suka shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar sakamakon kin amincewa da matakin gwamnan na Kaduna na korar ma’aikata fiyeda dubu biyu lamarin daya tsayar da jihar cak ta fannoni tattalin arziki da zamantakewa.


To Sai dai a rana ta biyu ta yajin aikin, Gwamna El Rufa’i ya sake korar ma’aikatan lafiya na jihar daga matakin albashi na 14 zuwa kasa.


Ana dai cigaba da sulhuntawa tsakanin gwamnatin jihar kadunan da kungiyar kwadago karkashin shiga tsakanin ministan kwadago da nagartar aiki Dr Chris Ngige.

3 COMMENTS

  1. Wan nan zan chan ba gaskiya bane
    Sai dai kawai baya san laifin da yayi a zar geshi shi kadai
    Wan nan shine dalili

    • Yanada kyau mai girma gwafnan kaduna ya it’s bakinsa Kuma ya shiga taitayinsa na sanin irin maganganun da zai furta akan bananmu naganin kukanmu adalin gwafnan Dr. Abdullahi Umar Ganduje domin ba sa’ansa bane nayi tsammanin ma zai nemi shawarar mai girma khadimul islam Yaya zaiyi ya iya biyan maikatan jahar kaduna albashi duk wata? Kokuma yace mai girma gwafnan Kano ya taimaka masa da bashin wasu kudi amma kwatsam sai ya fara surutai marasa tushe balantana makama daga karshe ina mai baka shawara daka gaggauta janye kalamanka daga ka mai girma adalin gwafnan Kano kafin musaka kafar wando daya da kai

  2. Wannan ya fara nuna yadda siyasar shekarar 2023 zata dauki dumin, kasancewar ko wanne cikin na kokarin buna kulaficin sa kan kujerar mataimakin shugaban kasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...