Yan Sanda Sun Kama Masu Yan Bindiga har guda 5 a Zamfara

Date:

‘Yan sanda a Jihar Zamfara sun kama mutum biyar da ake zargi da aikata fashi da garkuwa da mutane da mallakar makamai ba bisa a’ida ba.

Kakakin ‘yan sanda a jihar, Shehu Mohammed, shi ne ya bayyana su ga manema labarai a yau Juma’a a hedikwatar rundunar da ke Gusau babban birnin jihar.

Daga cikin mutanen har da wani da aka bayyana a matsayin ɗan ƙasar waje. Mutumin ya ce ya sayar wa da ‘yan fashi bindiga aƙalla 450.

Ya ce an yi nasarar kama su ne sakamakon haɗin gwiwa da suka yi da ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah rashen jihar ta Zamfara.

Waɗanda aka kama ɗin, rahotanni sun bayyana cewa su ne ke addabar garuruwa da dama a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina, inda suke kashe mutane tare da kama wasu don karɓar kudin fansa.

Shehu ya ce rundunar za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran ƙungiyoyin da ke da niyyar ba su gudummawa wajen inganta tsaro a jihar.

134 COMMENTS

  1. Бій Усик – Джошуа 25 вересня 2021 року на стадіоні “Тоттенхем” в Лондоні пройде супербій між українцем Олександром Усиком і чемпіоном світу з Великобританії Ентоні Джошуа. Anthony Joshua vs Oleksandr Usyk Усик Джошуа — скільки зароблять боксери за бій 25.09.2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...