Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Wata Kungiyar Tallafawa Mata da Marayu Mai Suna Orphans and Women Support Initiative ta ta dauki Gabarar Taimakawa Talaka da Marayu A Fadin Nigeria, Kuma Tuni Suka Fara da Jihar Kano kasancewar Masu Kungiyar Yan asalin jihar Kano ne.
Cikin Wata sanarwa da Babban Jami’inta dake kula da Arewa Maso yammacin Kasar nan Sadeeq Ali Dakata Aikawa ya Sanyawa hannu Kuma ya aikowa Kadaura24 yace Shugaban Kungiyar ba Kasa Hon. Baba Yawale ne ya bayyana hakan Yayin kaddamar da rabon kayan Sallah a nan Kano.
“Wannan NGO Yana Cigaba Da Rabawa Mabuqata Kayan Sallah Domin Faran Ta Musu Cikin Zuciyarsu Muna Rokon Allah Yasa Alheri Acikin Wan Nan Aiki”. Inji Ambassador Baba yawale
“Wan Tallafi Irin Aikin Da Allah Yakeso Ne Shiyasa Muke Shiga Kauyukan Da Kammu domin mu raba Kayan domin Neman yardar Allah”. Inji Shi
Amb. Baba Yawale yace Kalla Fiye Da Mutum Dari Biyar (500) Zasu Amfana da Wannan Tallafin,. Ya kuma ce Kofar su a Bude Take Ga Mai San Saka Hannu Jarin Da Babu Faduwa A Ciki Domin Samun Babban Rabo A Lahira.
Sanarwar tace Wanan Aiki da Kungiyar take gudanarwa Babu Ko koban wani Dan Siyasa “Mai Girma DG Wannan Kungiyabda Bata gwamnati ba NGO Shine Yake Daukar Nauyi Tare Damu Masu Taimaka Masa, Muna Da Shirye-Shirye da dama domin tallafawa Al’umma Daban-Daban”