Sabon Shugaban Kwamitin Riƙo na APC, Gwamnan Jihar Naija, Abubakar Sani Bello, ya kira taron gaggawa na shugabannin jam’iyar na ƙasa.
A wata sanarwar taron da ya sanya wa hannu da kan sa, tare da kuma Ken Nnamani (Kudu-maso-Gabas), Stella Okotete (Shugabar Mata ta Ƙasa), Sanata Aba Ali (Arewa-maso-Yamma) da kuma Farfesa Tahir Mamman (Arewa-maso-Gabas).
A sanarwar, za a yi taron ne ta yanar gizo a ranar 17 ga watan Maris da misalin ƙarfe 11 na safe.
An yanke hukuncin yin taron gaggawar ne a taron kwamitin riƙo km jam’iyar karo na 26 da ya gudana a ranar Talata.
Sanarwar ta ce an kira taron gaggawar ne ta la’akari da sashe na 25B (i da ii) na kundin tsarin mulkin APC da kuma ikon da a ka baiwa Kwamitin Riƙon a taron da a ka cimma matsaya a kan hakan a ranar 8 ga watan Disamba, 2020.