Buhari ne yace a cire Mai Mala Buni daga shugabancin jam’iyyar APC – El-Rufa’i

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya goyi bayan cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko na APC kamar yadda gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana.

A hirar da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi ranar Talata, El Rufai ya ce gwamnan Neja Sani Bello ya samu goyon bayan Buhari da kuma gwamnonin APC 19.

Sannan ya ce Buhari ne ya ce a cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni.

Buhari ne ya bayar da umarnin a cire shi kuma aka aiwatar, yanzu gwamna Bello ne ya gaje shi,” kamar yadda El Rufai ya bayyana.

Ya ce Mai Mala Buni wanda ba ya ƙasar zai dawo ne a matsayin gwamnan Yobe amma ba matsayin shugaban jam’iyyar APC ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...