Daga Sayyeed Abubakar
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullah Umar Ganduje ya yabawa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa yadda yake kyautata alaka Tsananin Gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kano Dama Masarautar Kano.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne Jim kadan da kammala Shan Ruwa da Mai Martaba Sarkin Kano ya Shiryawa gwamnan da Yan tawagarsa a fadar Masarautar Kano.
Gwamna Ganduje yace yadda Sarkin yake zaune lafiya da kowanne rukuni na al’umma Yana taimakawa wajen karawa Masarautar Kano da jihar Kano kima a idanun Duniya.
“Muna jin Dadin yadda kake zaune lafiya da Malamai da Yan Kasuwa da attajirai da Sauran al’ummar jihar Kano, Babu shakka kana koyi da Mahaifin ka Marigayi Sarkin Kano Dr Ado Bayero” . Inji Ganduje
“Gwamnatin Tarayya ta na jin Dadin yadda kake sa malamai suke yiwa Shugaban Kasa Muhd Buhari addu’a da Kuma yadda kake sawa ake yiwa Kasa da jihar Kano addu’o’in samun Zaman lafiya”. Inji shi
Gwamna Ganduje ya Kuma bukaci Sarki da yasa ayi addu’o’i na musamman domin ayi Haye-Hayen Sallah karama lafiya ba tare da wata matsala ba, sa’annan ya godewa Sarkin na Kano bisa karramawar da yayi Masa na shirya Masa liyafar Shan Ruwa a Wannan Wata Mai Albarka.
A Jawabinsa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa Gwamnan bisa amsa gayyatar da yayi ,Sannan ya baiwa gwamnan tabbacin Masarautar Kano zata cigaba da hada Kai da gwamnatin jihar wajen Kawo wa al’umma ci gaba.
Kadaura24 ta rawaito Mai Martaba Sarkin ya baiyana dadaddiyar alakar dake tsakanin Masarautar Kano da gwamnati Inda yace ba za’a samu cigaba ba matukar akwai sabani tsanin Gwamnati da Masarautar.