Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya karbi ragamar tafiyar da jam’iyyar APC bayan tsige Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe wanda ke jagorantar kwamitin riko na jam’iyyar a shekaru biyu da suka gabata.
A halin yanzu Bello yana jagorantar taron kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar APC na rikon kwarya da shugabannin jam’iyyar na jihohi.
Rahotannin sun nuna cewa a halin yanzu Mai Mala Buni Buni yana kasar waje.