Daga Salisu Kabiru Sakkwato
Yayin da tsohon Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ke fuskantar zafin kaye da ‘kungiyarsa ta G7 a cikin jam’iyyar APC a Jihar Kano, sakamakon hukuncin Kotun Daukaka Kara, sai kuma kwatsam ga jam’iyyar APC din daga Jihar Sakkwato garin Shehu su na jan kunne mai tsanani game da yadda Malam Shekarau ke sanya baki cikin al’amuran jam’iyyar a Jihar.
A wata sanarwa mai kama da gargadi na karshe ga Malam Shekarau din, Shugaban jam’iyyar APC na Sakkwaton Hon. Isa Sadiq Acida ya yi tir da wani yunkuri da Sanata Ibrahim Shekarau ke yi don ganin an ruguza jam’iyyar a jihar.
Tare da cewa za su tabbatar an dakile wannan mugun nufi kamar yadda a ka yi wa kungiyar “Banza Bakwai” a Kano.
Wannan gargadi ya yi shi ne a shafin jaridar Daily Trust shafi na 29, ta ranar Talata 1 ga Watan Maris, na wannan shekarar.
Gaskiya wannnan jan kunne abun a yaba ne, kasancewar jam’iyyar tana karkashin jagorancin tsohon Gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko, sannan akwai dukkanin Sanatocin jihar da daukacin ‘yan Majalisar Tarayya da Ministan Harkokin ‘Yan Sanda da Jakadun kasashen waje.
Ragowar wadanda ke tare da wannan shugabanci sun hadar da ‘yan Majalisar Dokoki na jihar da tsofaffin mataimakan gwamnoni da tsofaffin ‘yan majalisa da kuma dukkan wasu masu fada a ji a jam’iyyar a Jihar ta Sakkwato, wanda hakan ke nuna cewa kan ‘ya’yan jam’iyyar a hade yake.
Idan Malam Ibrahim Shekarau ya na jin cewa ya na da wata kwarewa a siyasa, to sai ya koma Jihar Kano ya yi amfani da wannan kwarewar tasa ya karbi ragamar jagorancin jam’iyyar ta APC a Kanon, amma ba yazo jihar mu ta Sakkwato ya yi ta kai-kawo domin ruguza mana jam’iyya ba
Siyasar jihar Sakkwato tana da banbanci da ta jihar Kano, don haka Shekarau bai isa ya kawo rudu a APC ba a Jihar Sakkwato. Idan kuwa ya ci gaba da haka, to tabbas a nan ma zai sha kashi irin na siyasa kamar dai yadda kungiyar sa ta Banza Bakwai ta sha kashi a Kano.”
A Jihar Sakkwato fa kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a hade yake waje guda. Saboda haka ba wani gangamin masu makirci da zai rusa jam’iyyar a Jihar.
Duk wani mai kishin jam’iyyar APC a jihar Sakkwato zai yi maraba da wannan matakin gargadi ga Malam Shekarau da shugabancin jam’iyyar APC na jihar ya dauka, domin kuwa zai kara dakushe yunkurin da Malam Shekarau ke da shi na zama wani mai fada a ji a cikin jam’iyyar.
Haka kuma, uwar jam’iyyar ta kasa za ta dauka cewar Malam Shekarau din tamkar ya Sha alwashin ruguza jam’iyyar ne a wannan sashin na Arewa Maso Yamma.
Yanzu abin ya zamewa Malam Shekarau gaba kura baya sayaki.
Salisu Kabiru Sakkwato, Dan gwagwarmayar siyasa a jihar Sakkwato, za’a iya samu na a wannan adireshi skabiru@gmail.com