Daga Sani Abdulrazak Darma
An bukaci sabbin Shugabannin Kungiyar ‘yan Tifa na Jihar Kaduna da su zamo masu gaskiya da Adalci da kuma aiki tukuru.
Bayanin Hakan ya Fito ne ta bakin guda daga cikin Iyayen Kungiyar na kasa Reshen Arewa Alh Husaini Adamu, yayin Rantsar da Sababbbin Shuwagabannin Kungiyar ‘yan Tifa ta Kasa reshen Jihar Kaduna.
Alh Husaini Adamu yace sana’ar Tifa a bace wacce take da albarka da kuma taimakawa wajen samar da aikin yi ga matasa tare Kuma da bunkasa tattalin Arzikin kasa.
Adamu ya bukaci Sababbbin Shuwagabannin Kungiyar ta ‘yan Tifa na Kaduna da su rinka yiwa ‘ya’yan Kungiyar bita akai-akai domin kaucewa fadawa cikin wata matsala.
Alh Husaini Adamu ya godewa gwamnatin Jihar Kaduna data Sanar da fili kyauta ga Kungiyar Direbobin Tifar, da kuma basu damar yin amfani da Filin bisa ka’ida.
Tun da fari a nasa jawabin Sakataren Kungiyar ‘yan Tifa na Jihar Kano Wanda ya wakilcin Shugaban Kungiyar Commared Mamuni Ibrahim Takai, ya ja hankalin Direbobin dasu zamo masu biyayya, da kuma yin tuki batare da ganganci ba.
Yayin da yake Jawabin sa bayan ya karbi Rantsuwa Sabon Shugaban Kungiyar Commared Muhd Sani Ja’afar ya bayyana farin cikin sa, inda ya yi kira ga duk masu tuka motar Yashi, Kasa, Dutse dasu bashi hadin kai domin ciyar da Kungiyar gaba.
Sani Ja’afar yace zai iya bakin kokarinsa domin Samar da cigaba a Kungiyar tare da yin Adalci ga kowa.
Wakilin Kadaura24 daga can Jihar ta kaduna ya rawaito mana cewar tarony ya samu halartar Jami’an dake kula da hanya na Kaduna, da kuma Jami’an tsaro daga kowane bangare domin tabbatuwar lamarin.