Kungiyar cigaban Unguwar Adakawa dake K/H Dala ta Shirya taron wayar da kan Matasa illar Shaye-shaye

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Kungiyar cigaban unguwar Adakawa da kewaye dake Karamar Hukumar Dala ta sha Alwashin yaki da munanan ayyuka a tsakanin matasan yankin .

Kadaura24 ta rawaito Shugaban kungiyar Suleiman Bala Ibrahim shi ne ya bayyana hakan yayin taron da kungiyar ta shirya domin wayar da kan matasan game da matsalolin shaye-shaye da wasu daga cikin matasa ke fama dashi.

Sulaiman Bala yace shaye-shayen miyagun kwayoyi na taka muhimmiyar rawa wajen haifar da ta’addanci a tsakanin matasa, Inda yace idan aka sami nasarar magance matsalolin shaye-shaye za a Kawo karshen ta’addanci a Ƙasar nan.

Yace Kungiyar tana iya Bakin kokarin ta wajen Magance shaye-shaye ta fuskar wayar da Kan Matasa su fahimci illar da shaye-shayen ke haifar ga shi Mai Sha da kuma al’umma baki daya.

Da yake jawabi wakilin hakimin Dala sayyidi Mahmud Nura ya bukaci iyaye da su maida hankali wajan kula da tarbiyyar ‘ya’yansu domin ta hakane zasu samar da ingantacciyar al’umma abar alfahari.

Ya bayyana cewa wajibine akan iyaye su baiwa ‘ya’yansu ilimi da tarbiyyar kamar yadda addinin musulunci ya yi umarni domin ‘ya’ya amanace da Allah ya sanya a hannun iyaye kuma zai tambayesu yadda suka gudanar da ita.

Daya daga cikin iyayen kungiyar malam umar Adakawa ya bukaci mawadatan dake yankin dasu tallafawa wannan kungiyar domin ganin ta cimma burin data sanya a gaba na tallafawa rayuwar yan uwansu matasa a fannoni daban daban na rayuwa domin samun al’umma ta gari.

Taron ya samu halarta Jami’an tsaro yan kasuwa da dukkanin masu ruwa da tsaki dake yankin, taron wanda ya gudana a zauren sharifai dake Adakawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...