Hotuna na da Aisha Humaira ba na aure ba ne, na talla ne – Inji Mai-shadda

Date:

Fitaccen Mai tsara fina-finan Hausa na Kannywood, Abba Bashir, wanda a ka fi sani da Mai-shadda ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa cewa zai auri jaruma Aisha Ahmad, wacce a ka fi sani da Aisha Humaira.
A yau Alhamis ne dai Kadaura24 ta rawaito cewa Mai-shadda na daf da angwance wa da Aisha Humaira, bayan da ya wallafa hotunan da su ka ɗauka tare a shafinsa na Instagram.
“Zan yi wuff da gishiri ambassador.”, haka Mai-shadda ya rubuta a saman hotunan da ya wallafa a Instagram ɗin.
Bayan wallafar da ya yi, jaruma Aishat Humaira ta sake wallafa hotunan a shafinta na Instagram, inda ta haɗa da alamar soyaiya.
Hakan ne ya sanya a ka dinga yayata wa cewa aure jaruman na Kannywood za su yi.
Sai dai kuma wata majiya da ke kusa da Mai-shadda, a yammacin Alhamis ta shaida wa Daily Nigerian Hausa cewa hotunan ba na aure ba ne, na talla ne.
A cewar majiyar, jaruman biyu sun ɗauki hotunan ne domin yi wa Kamfanin Shehu Danƙwarai da ke kasuwar Kantin Kwari.
Majiyar ta ce nan ba da daɗewa ba Mai-shadda zai wallafa tallan a shafinsa na Instagram.
“in an jima kaɗan ma zai saki tallan a kan Instagram ɗin shi sabo da mutane su na ta damun shi da waya.
“Tallan Kamfanin Shehu Danƙwarai ne, in an jima zai sanya shi a Instagram,” in ji majiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...