Halima M Abubakar
Kungiyar malamai ta Najeriya reshen karamar hukumar Gwale ta bayyana nadin Malam Mustapha Adamu sabon jami’in kula da Tsangaya na Jihar kano a matsayin wanda ya dace.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar reshen karamar hukumar Kwamared Auwalu Shuaibu Ja’e kuma aka aikowa Kadaura24.
Sanarwar ta kuma bayyana Malam Mustapha Adamu a matsayin jami’i mai kwazo da sadaukar da kai wajen bunkasa ilimi a kananan hukumomi da jiha baki daya. .
Sanarwar ta ce kungiyar ta yabawa gwamnatin jihar bisa wannan nadin da kuma kokarin da take yi na inganta fannin ilimi a jihar kano.
Malam Mustapha Adamu har zuwa lokacin da aka nada shi, shi ne Shugaban sashin Larabci a Hukumar Ilimi ta Karamar Hukumar Gwale.