Ganduje ya samar da dakunan karatu a k/h 44 ne don cusawa dalibai dabi’ar karatu – Hafsat Ganduje

Date:

Daga Maryam adamu Mustapha
Gwamnatin jihar kano ta bayyana aniyarta na cigaba da bunkasa dakunan karatu wato library dake Jihar nan, domin bunkasa fannin ilimi tare da bukatar daliban dasu kasance masu gudanar da bincike da karatuttuka domin cigaban karatunsu
Kadaura24 ta rawaito Maidakin Gwamnan Jihar kano farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje ce ta bayyana hakan yayin bada shaidar kammala daukar horo na ilimin na’ura mai kwakwalwa a fannoni daban-daban na mata da maza kimanin su 131 Wanda aka gudanar a dakin karatu dake jihar nan.
Mai dakin gwamnan tace hakanne ma yasa gwamnatin jiharkano ta Samar da dakunan karatu a kananan hukumomin jihar 44 don bunkasa Karatun dalibai da Kuma cusa musu dabi’ar yin Karatu.
Farfesa Hafsat Ganduje ta kara da cewa rashin maida hankali wajen karatun dalibai shi ke Kawo musu koma baya a sha’anin Karatun, a don haka ta bukaci iyaye dasu tashi tsaye wajen ganin ‘ya’yansu sun sami ilimi mai nagarta. Ta kuma  bukaci daliban Jihar Kano da su kasance masu nacin karatu musamman a dakunan karatun da ake dasu domin bunkasa harkokin ilimi aj ihar dama kasa baki daya .
Farfesa Hafsat Ganduje ta bukaci daliban da suka sami horon da suyi amfani dashi yadda ya dace duba da cewa a yanzu haka an zamanantar da harkar karatu ta fannin na’ura mai kwakwalwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Dalilin da ya hana Sarki Aminu Ado Bayero zuwa gidan yari na goron dutse a yau alhamis

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin...

Matakai 3 da gwamnatin Kano ta dauka kan kafafen yada labarai a jihar

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnatin jihar Kano ta ce a...

Yadda manoma a Kano suka zargi jami’an Civil defense da karbar kudade a wajensu

Daga Umar Ibrahim kyarana   Manoman dajin dansoshiya dake karamar hukumar...