Daga Aisha Aliyu Muhd
Mawakin nan Naziru M Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya Kalubalanci yan Kanywood da tauye hakkin Ma’aikatan Cikin masana’antar Musamman tsofaffi da Mata .
Kadaura24 ta rawaito Nazir M Ahmad ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo, jim kadan bayan Ali Nuhu da Falalu A Dorayi sunyi wa Hajiya Ladin Cimma Haruna Martani kan kudin da ake ba ta a fim.
Yace Abun da dattijuwar can ta fada gaskiya ne…. Dubu biyu dubu ukku Ake bawa dattawa Yan film,don haka kumarta huta Kar kusa Wata cutar ta kamata.
Sannan yace ya Rantse da Allah Haka Akeyi Idan kuma Akwai Wanda ya Isa yazo ya Musu to Yana jira.
“Na taba Kiran Wata dattijuwa Aikin fim Bayan ta Gama na dauki kudi na bata Kawai sai matar nan ta rikice tana yimin godiya Kamar ta yimin sujjada ,sai na tambaya ya haka sai aka ce ai Dubu biyu Dubu uku ake basu Yau Kuma ta ji Dubu 10 a hannunta shi yasa ta rikice”. Inii Nazir m Ahmad
Sarkin Waka ya ce ana cin zarafin wasu daga cikin mata ta hanyar lalata da su saboda za a sanya su a fim, wayansu kuma a kyauta hasali ma sune zasu biya kudi a sanya su.
“Duk da bana harkar fim sosai Amma nasan akwai wacce Magana ta Ladin cima, Sannan Muna sane da yadda Wasu ma maimakon a biyasu in an saka su a fim sai dai su su biya Wasu Kuma Yan Matan ayi lalata dasu kafin a saka su a fim din Wannan Kowa ya Sani”. Inji Sarkin waka
Ya ce masana’antar tana samun nakasu, kuma ya kalubalanci duk wadanda suka karyata zancen hajiyar da cewar su yi rantsuwa kan abunda da ta fada ba gaskiya ba ne.
Naziru ya kalubalanci ali nuhu da Falalu A Dorayi bisa take gaskiya kan furucin su, ya ce zasu iya musa masa kan kalaman da ya fada idon karya ne ba’a aikatawa.
Sai dai shi ma a safiyar Ranar Juma’ar nan Mai Shirya fina-finan Hausa nan Abubakar Bashir Mai shadda ya Mayar Masa da Martani tare da Karyata dukkanin kalaman Nazirun.