IPMAN ta nemi afuwar al’umma bisa sayar musu da gurbataccen Man fetur

Date:

Daga Hamida Nasiru

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, ta nemi afuwar jama’a kan sayar da gurbataccen mai da mambobinta suka yi a fadin kasar.

Kadaura24 ta rawaito Shugaban kungiyar IPMAN reshen Kano, Alhaji Bashir Danmallam ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Talata.

Ya ce kungiyar ta ga ya dace ta nemi afuwar jama’a bayan da ta gano cewa man da ‘ya’yanta suka sayo daga Legas da Warri da sauran wurare gurbataccene Kuma an sayarwa al’umma shi.

“Mambobin mu sun sayi kayan ne daga Legas, Warri da sauran wuraren da aka ajiye ba tare da sanin gurbatattu bane.

“Don haka, mun ga ya dace mu nemi afuwar jama’a kan lamarin domin kada a zargi mambobinmu domin ba laifinsu ba ne,” in ji shugaban IPMAN.

Sai dai ya zargi jami’an gwamnati da ke aiki a dakunan gwaje-gwaje da rashin sanar da mambobinsu Cewa man gurbatattune.

A cewarsa, jami’an da ke aiki a dakunan gwaje-gwajen na da hurumin gano gurbatattun Mai tare da sanar da mambobinsu don kada su saya su sayar wa jama’a.

Dan Malam ya bayyana cewa kungiyar ta tuntubi Manajan Daraktan Kamfanin Tallan Kayayyakin Man Fetur (PPMC), Mista Isiyaku Abdullahi wanda tun a lokacin ya umarci duk ‘yan kasuwar da suka sayi gurbataccen samfurin da su mayar da shi inda suka saya.

Danmalam ya bada tabbacin cewa IPMAN za ta hada kai da mahukuntan kamfanin man fetur na kasa (NNPC) domin hana afkuwar afkuwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...