Daga Sani Sadiq kk
Wasu jiga-jigan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da kungiyoyi zasu kaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa a mako mai zuwa, Kamar yadda Jaridar Vanguard ta rawaito.
Kadaura24 ta rawaito Wadanda ake sa ran zasu kafa wannan sabuwar tafiya sun hada da:
1. Prof Pat Utomi 2. Dr Usman Bugaje 3. Engr Musa Rabiu Kwakwanso, 4. Farfesa Kingsley Moghalu, 5. Sanata Saidu Dansadau, (Shugaban, NRM) 7. Hadjia Najatu Mohammed, 8. Prof Remi Sonaiya, 9.Pastor Ituah Ighodalo, 10. Prof Osita Ogbu; 11. Dr Sadiq Gombe; 12. Comrade Promise Adewusi; 13. Chief Akin Braithwaite; 14. Arc Ezekiel Nya Etok; 15. Lady Khadija Okunnu-Lamidi; 16. Comrade Olawale Okunniyi dss.
Yan siyasar sun yanke wannan shawarar ne a taron samar da sabuwar jam’iyyar da zatayi fito-na-fito na jam’iyyun PDP da APC ranar Lahadi a Legas.
Jam’iyyu da kungiyoyin da suka hallara sun hada da Rescue Nigeria Project, RNP; Nigeria Intervention Movement, ÑIM; Strategic Elements of the Civil Society Movement; Youths’ EndSars Movement, National Rescue Movement, NRM; da African Democratic Congress, ADC.
Yan bangaren Osinbajo sun tuntubi Kwankwaso
Hakazalika an rawaito cewa wasu yan bangaren mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sun tuntubi Kwakwaso, duk da cewa Osinbajo bai bayyana aniyyarsa ba tukunna.
Rahotannin sun bayyana cewa wasu yan bangaren mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sun tuntubi Kwakwaso, duk da cewa Osinbajo bai bayyana niyyarsa ba tukun.
Wata majiya mai karfi tace har Shugaban jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya yi kira ga Kwankwaso domin ya koma APC. A cewar majiyar: “Tattaunawa na gudana tsakanin Oga da su.
Suna son ya dawo APC amma ana shawara kai. Ba a yanke ba.”