Yanzu Yanzu: APC ta sake kiran Ganduje da Shekarau taron gaggawa

Date:

Daga Zakariyya Adam Jigirya
 Shugaban kwamitin rikon jam’iyyar APC Mai Mala Buni, ya sake kira taron gaggawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Kano.
 Wadanda aka gayyata taron sun hada da Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau da wasu fitattun masu ruwa da tsaki daga ko wane bangare na bangarorin biyu.
Kadaura24 ta rawaito a taron na ranar Juma’a, bangarorin biyu sun gabatar da buƙatunsu a gaban shugabannin jam’iyyar na Kasa yayin Zaman sulhun.
 Wasu majiyoyin daga wajen taron sun ce gwamnan ba ya son baiwa tsagin Shekaru Manyan mukamai a  jam’iyyar, Amma dai ya bukaci su Shekarau su bada sunayen wadanda suke so domin ya basu mukamai a gwamnatinsa.
 APC ta Kano ta Sami kanta a wannan ne sakamakon rikicin da ya barke tsakanin bangaren Gwamna Ganduje da bangaren Malam Shekarau.
 Rikicin dai ya kai ga gudanar da gudanar da zaben Mazabu dana kananan hukumomi da na jiha, inda Abdullahi Abbas ya zama shugaban jam’iyyar na jiha tsagin Ganduje da Ahmadu Danzago daga tsagin Malam Shekarau.
 Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, Dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar birni, Shaaban Sharada Shi ne yake daukar nauyin duk Wannan shari’u da zabukan da tsagin Shekarau sukai.
 A halin yanzu dai ana gudanar da taron ne a masaukin Gwamnan Yobe dake Asokoro Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...