Wata kungiya a Kano ta kai tallafi ga daurarrun dake gidan gyaran hali na kurmawa

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

 

Wata kungiya Mai suna youth mobilisation by media ta kai ziyara zuwa gidan gyaran hali da tarbiya na kurmawa domin tallafawa fursunonin Gidan da abubuwan bukata na yau da kullum.

Kadaura24 ta rawaito yayin ziyarar kungiyar ta rabawa dauraru mata da maza kayiyyaki Masu tarin yawa wanda suka hada da magi, omo da kuma kayansawa na maza da Mata.

Shugaban wannan Kungiya comrade Salisu Gambo Detol yace sun kawi ziyara gidan na kurmawa ne domin tunawa da yan uwa da suke tsare a gidan gyran halin don a basu Gudunmawa la’akari da halin da suke ciki.

 

Sakon taya Murnar Samun shugabancin jam’iyyar SDP a Jihar Kano.

Comrade Salisu yace dama Lokaci zuwa lokaci Kungiyar su tana bada irin wannan tallafi don taimakawa gwamnati kasancewar ba zai yiwu ace komai an barwa gwamnati ba.

Ya jajantawa daurarrun Saboda halin da suka tsinci Kansu a ciki tare da fatan zasu zama jakadu na gari a duk inda suka tsinci Kansu bayan sun kammala Zaman Gidan tare Kuma da gujewa Kara aikata laifin da Zai sa a sake mayar da su gidan.

 

Wasu daga Cikin Waɗanda suka amfana da tallafin sun nunu farin cikinsu da godiyarsa bisa tallafin da Kungiyar ta Kai musu, tare da yin Kira ga Sauran Kungiyoyi da suyi koyi da abun alkhairin da Kungiyar da yi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Na sauke nauyin da Tinubu ya ɗora min – Gwamnan riko na jihar Rivers

Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai ritaya), wanda shi ne gwamnan...

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...