MAAUN Ta Taya Farfesa Rayyan Muhammad Garba Murnar Cika Shekaru 40 Da Haihuwa

Date:

Daga Ali Kakaki

Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya taya Farfesa Rayyan Muhammmed Garba murnar cika shekaru 40 da haihuwa.

Farfesa Rayyan Muhammad Garba shi ne Daraktan Tsare-tsare na Ilimi a Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijar.

Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo kuma aka aikewa mai bikin.

Farfesa Gwarzo, wanda har wala yau shi ne Shugaban kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu a Afirka, ya bayyana Farfesa Rayyan a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana wanda ya himmatu wajen ganin matasa musamman daga Arewacin kasarnan musamman Nijeriya baki daya sun samu ilimin kimiyya da ilimin kirkira.

Ya kuma bayyana mai bikin a matsayin abin koyi ga matasa masu mutunta Dattijai a cikin al’umma da kuma masu son su yi nasara a abin da suka zaba a rayuwa.

“A don haka bisa la’akari da wadannan halayya da aka ambata kan wanda ake taya murna, ina taya ka murnar cika shekaru 40 a duniya a madadin Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha da Jami’ar Franco-British.

“Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da yi muku albarka, ya kuma ba ku kwarin guiwa domin ci gaba da samar da ingantaccen ilimi a fanninku na musamman kan ilimin kimiyya da fasaha ga dalibanmu,” inji Farfesa Abubakar Gwarzo.

Dr Rayyan Garba kwararren likita ne kan kiwon lafiyar Jama’a kuma Farfesa ne a bangaren kiwon lafiyar al’umma. Ya samu nasarar gurbin karatu kyauta ta ‘British Commonwealth’ domin karatun digiri na biyu kan nazarin kiwon Lafiyar Jama’a a Makarantar Tsafta da magunguna ta Landan wato ‘London School of Hygiene and Tropical Medicine’.

Ya halarci tarukan horaswa na kasa da kasa da yawa ciki har da horo kan zane-zane da ci gaba, a Makarantar Rollins na Kiwon Lafiyar Jama’a, Jami’ar Emory a Atlanta Georgia dake Amurka; da kuma horo na 10 kan ‘Alurar rigakafi domin Afirka’ a Jami’ar Cape Town dake Afirka ta Kudu.

Ya aiwatar da shirye-shirye da ayyuka masu yawa na kiwon lafiya na kasa da kuma na abokan ci gaba da ake da huldar alaka da su da kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda suka hada da Hukumar Lafiya ta Duniya, USAID, DFID, NPHCDA da sauransu.

Dakta Rayyan ƙwararren mai bincike ne wanda ya gudanar da bincike na ƙasa, kuma ya buga makalu a cikin gida da waje a cikin mujallun da ake bitarsu kan batutuwa daban-daban da suka shafi lafiyar jama’a a yau.

Har wala yau, ya yi bitar makalu da dama da aka buga a mujallun ilimi na gida da na waje a fannin kiwon lafiyar duniya, ciki har da BMC Public Health, PLoS ONE, Alurar Dan Adam da Ilimin Lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...