Sabon Rikici ya kunnu Kai Tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Date:

A daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yin sulhu tsakanin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da magajinsa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wani sabon rikicin siyasa ya sake kunno kai tsakaninsu.

Yayin wata hira da jaridar Punch a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana nasarar da Ganduje ya samu a zaɓen 2019 a matsayin haramtacciya, yana cewa wasu gaggan ƴan siyasa ne daga sama suka ƙaƙaba wa al’ummar jihar Kano shi.

“Sun tursasa wa ɗumbin mutane ra’ayin wasu ƴan tsiraru wanda hakan shi ne laifi mafi muni a tsarin dimokuradiyya. Ina tsammanin sun fahimci kuskurensu a yanzu, wasunsu na ƙoƙarin gyara kura-kuransu a yanzu bayan barnar da aka yi wa jihar Kano. Abin takaici ne yadda suka kasa ganin abin da talakawa suka hango wa kansu.”

Ya ci gaba da cewa ”Muna da ƙarfin da za mu iya hana su abun da suka so yi a wannan lokaci, amma muka buƙaci matasanmu su kwantar da hankalinsu, muka bar su da aniyarsu, muka bi matakin shari’a, amma a nan ma aka yi abun da aka yi” in ji Kwankwaso.

Martanin Ganduje

Sai dai wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin jihar Kano mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Watsa Labaran jihar Muhammadu Garba, ta bayyana kalaman na Kwankwaso a matsayin shaci-faɗi da ko kaɗan babu ƙanshin gaskiya a cikinsu.

”Abun takaici ne yadda a matsayin Kwankwaso na shugaba, wanda ake damawa da shi a harkokin gudanar da zaɓe ya kasa amincewa da sakamakon zaɓen da hukuma mai zaman kanta ta gudanar kuma kotu ta amince da shi” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta Kano ta ci gaba da cewa hirar da Kwankwason ya yi da jaridar Punch ta janyo masa mummunar illa ne fiye da alfanun da ya yi tsammanin za ta haifar masa.

A cewarta a fili take cewa Kwankwaso ya fahimci gwamnatin Ganduje ta tsere wa sa’a wajen shimfiɗa muhimman ayyuka ga jama’a, shi ya sa yake ganin ana ƙoƙarin shafe abun da yake ganin ya yi a nasa

”Kwanan nan aka ji shi ya jan hankalin magoya bayansa su kaucewa furta miyagun kalamai amma sai ga shi ya ɓige da yi shi da kansa, ko kaɗan wannan bai dace da shi ba”, a cewar sanarwar

1 COMMENT

  1. Abinda kwankwaso ya fada tabbas gaskiya ne amma kamata yayi ya jure tunda ana maganar sulhu.

    A jawabin martani kuma nayi mamakin yadda maganar kotu ta shigo ciki dubada yadda kotu tayi hukunci danganeda tabbatarda Alh Ahmadu Haruna zago a matsayin shugaban jamiyyar APC a matsayin shirme da zancen wofi kamar yadda tsohon shugaban ya bayyana

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...