Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa duka yan Najeriya bisa ƙarfin hali da juriya da suka nuna a shekarar da ta gabata ta 2021, sakamakon ƙalubalen da ƙasar ta fuskanta na annobar korona a daidai lokacin da kuma ake ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziki da samar da zaman lafiya.
A wani saƙon sabuwar shekara da shugaban ya aika wa ƴan ƙasar nan, shugaban ya bayyana karfin gwuiwarsa kan ci gaban da ake samu a bangaren tsaro duk da koma bayan da ake samu.
“Ina tabbatar muku cewa za mu ci gaba da zage damtse domin cika alkawuran da muka dauka na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.”
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta sauya takun da take yi ta hanyar nemo wasu hanyoyin da suka hada da sasanci da sulhu domin kawo karshen yaki kamar irin matsalolilin da ake fuskanta na barayin daji da kuma ‘yan Boko Haram a arewacin kasar, baya ga rikicin kungiyar IPOB a kudu maso gabashin kasar.
A bangaren tattalin arziki, jawabin shugaban na Najeriya ya tabo abin da ya kira, “juriyar da tattalin arzikinmu ya nuna duk da koma bayan da annobar korona wadda ta dabaibaye dukkan kokarin da kasashen duniya ke yi na gina kasa.”
Ya kuma ce tattalin arzikin Najeriya ya sami karuwar kashi 5 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2020 wanda ya ce ya fi na dukkan kasashen Afrika da ke kudu da hamadar sahara, kuma ya zarce na dukkan shekarun baya-bayan nan musamman tun 2014.
Ya kuma tabo batun sanya hannun da ya yi kan dokar Petroleum Industry Act mai zummar gyara lamurran hakowa da sarrafa albarkatun man fetur a kasar, inda ya gode wa Majalisun kasar saboda hadin kan da suka ba gwamnatinsa wajen samar da wannan dokar da ya ce an shafe kusan shekaru ashirin ana kokarin samar da ita.
BBC Hausa ta rawaito Shugaba Buhari ya sanar da ‘yan Najeriya cewa daga wannan shekarar, gwamnatinsa za ta rika rungumar fasahar sadarwa ta zamani a karkashin shirinta na samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar da bunkasa tattalin arziki.
Allah ya wa baba Buhari jagora,
Allah ka gafartamuna zunabban mu
Ya yaye muna matsalar tsaro awannan
Kasa tamu nigeria, da dukkan kasashen
Musulmi.