‎ ‎Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi

Date:



‎Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi II, ya bai dace gwamnatin Shugaban Kasa Bola tinubu ta ci gaba da ciyo bashi ba bayan ta cire tallafin man fetur.

‎Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Talata, a taron Oxford Global Think Tank Leadership da ƙaddamar da wani littafi, Sanusi ya ce cire tallafin man ya haifar da ƙaruwar kuɗaɗen shiga na gwamnati.

‎Sanusi ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi, yana mai bayyana matakan a matsayin “masu raɗaɗi amma na wajibi.”

FB IMG 1753738820016
Talla


‎Sai dai ya yi gargaɗin cewa waɗannan gyare-gyare ba za su yi tasiri ba sai an haɗa su da tsari mai kyau na kashe kuɗi da gaskiya a cikin gudanar da gwamnati.

‎“In ka daina biyan tallafi amma ka ci gaba da yin rance, hakan na nufin ka rufe rami guda ne sai ka buɗe wani. Kalubalen da ke gabanmu yanzu shi ne ingancin yadda gwamnati ke kashe kuɗi da kuma yadda ake tafiyar da kuɗaɗen da aka ce an ajiye,” in ji shi.

Shugaban Karamar Hukumar Ungogo Ya Raba Kwamfutoci Ga Daliban da Suka Samu Tallafin Karatu Zuwa Kasar Indiya

‎Sanusi, wanda ya jagoranci CBN daga 2009 zuwa 2014, ya ce matsalolin tattalin arzikin Najeriya a yanzu sun faru ne a sakamakon rashin daidaito a manufofi da siyasar neman sai an faranta wa jama’a da aka dade ana yi.

‎Ya yaba wa ƙwararrun da ke cikin tawagar tattalin arzikin gwamnati kan matakan da suka ɗauka don daidaita hauhawar farashi da rage canjin farashin kuɗi, amma ya jaddada cewa dole ne a dakile ɓarna da almubazzaranci cikin gaggawa.

‎Yayin da yake tambaya kan yadda gwamnati ke kashe kuɗi, Sanusi ya ce: “Me ya sa muke da ministoci 48? Me ya sa ake da jerin motocin gwamnati masu yawa? Me ya sa har yanzu ana yin rance bayan cire tallafi? In ka rufe rami guda, me ya sa za ka buɗe wani?

‎“Wannan gwamnati na bukatar ta duba hukumomi da yadda ake amfani da kuɗi a dukkan matakai. Domin in ka ci gaba da samun kuɗi amma kana kashewa ba daidai ba, za ka lalata duk wani ci gaba da aka samu.

‎“Amma irin mu da za mu ce, ‘Ya Shugaban Ƙasa, wannan ba daidai ba ne,’ ana ɗaukarmu a matsayin abokan gaba. Don haka, idan shugabanni sun kewaye kansu da masu yabon kai, ba za su taɓa samun shawara mai kyau ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...