Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba

Date:

 

Ƙungiyar tsofaffin kansiloli na jihar Kano ta gudanar da taron saukar Alƙur’ani mai tsarki tare da addu’o’i na musamman domin neman albarkar Allah ga Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, saboda biyansu hakkokinsu da gwamnatinsa ta yi a baya.

Shugaban ƙungiyar, Hon. Sanusi Kata Madobi, ya bayyana cewa wannan taro wani ɓangare ne na nuna godiya da jinjina ga gwamnan, wanda ya sauke nauyin da suka daɗe suna jira tun zamanin da.

 

” Ya Zama wajibi a gare mu mu yi Wannan taron domin nuna godiya ga Allah da ya baiwa mai girma gwamnan Kano damar biyanmu hakkokinmu, tabbas gwamnan ya sanya mu cikin farin ciki muna dole mu nema masa hakan a wajen Allah”. Inji Sanusi Kata

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Limaman Kwankwasiyya, Gwani Muhammad Sani Tilo, wanda shi ne limamin masallacin Ibadurrahman da ke Tudun Yola, ya jaddada muhimmancin yi wa shugabanni addu’a idan suka yi abin kirki ga al’umma.

” Yiwa shugabannin addu’a ibada ce kuma yana taimakawa shugabanni su sami basirar yiwa al’ummarsu hidima yadda ya dace, kamar yadda zaginsu ke karkatar da hankalinsu daga yin abun da ya dace”. A cewar Gwani Sani

Shi kuma Shugaban Majalisar Limamai na Jihar Kano, Imam Muhammad Nasir Adam na masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani Kofar Mata, ya yi kira ga gwamnan da ya ci gaba da biyan sauran hakkokin jama’a da su ke jiran gwamnati.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda shi ma jagoran ƙungiyar tsofaffin kansilolin ne, ya bayyana jin daɗinsa da irin haɗin kai da suka nuna, tare da tabbatar da cewa gwamnatin Kano ta kuduri aniyar biyan dukkan haƙƙin tsofaffin ma’aikata a matakai daban-daban.

Taron, wanda ya gudana a masallacin juma’a na Sheikh Ahmadu Tijjani, Kofar Mata, ya samu halartar malamai, limamai da sauran manyan baƙi, inda aka gudanar da saukar Alƙur’ani da addu’o’i na musamman domin neman cigaba da nasara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a jagorancin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla mutane...

Yadda ƴansanda suka kama wasu da suke zargin ƴanbindiga ne a Kano

Rundunar yansanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce...

Rikici a Bebeji: Jigon Kwankwasiyya na zargin an shirya cire sunayen tsoffin kansiloli domin yin kashe-muraba

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji...

KANFEST 2025: Gwamna Abba ya umarci sarakunan Kano da su ci gaba da hawan sallah

  Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarci...